No content on this channel :c try Try Looking at shorts maybe lol :p
Manufar bude wannan tashar ita ce raya al'adun illahirin kabilun Arewacin Kasar Hausa.
Arewacin Kasar Hausa na da kabilu guda 10 cif wadanda suka hada da:
1.Hausawan asali (Arawa, Gobirawa, Gubawa, Adarawa, Katsinawa, Damagarawa, Cangawa, Kabawa, Zamfarawa, Daurawa, Agadasawa da kuma Kurfayawa) kashi 54 cikin dari.
2.Zarma-Songhay-Dandawa kashi 22 cikin dari.
3.Abzinawa (Buzaye/Tuareg) kashi 10 cikin dari.
4.Fulani 8 %
5.Kanuri (Manga, Dagirawa, Bilma, Mobeur, Yerwa, Kanembu, Suwurti) kashi 5 cikin dari.
Sauran kabilun kasar Nijar sun hada da : Tasawakawa,Tagdalawa, Larabawa, Budumawa, Gurmawa da kuma Tubawa.
Kusan kashi 90 da 'yan kai cikin dari na al'umar Nijar na ji kuma na yin amfani da harshen hausa wajen gudanar da aiyukan yau da kullum. Abinda ke nufin cewa Hausa ce harshen da ya fi rinjaye kan duk wani harshen da ake amfani da shi a kasar. Kashi 99 ciki dari na Jamhuriyar Nijar Musulmai ne.